1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Asara saboda ta'addanci a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
September 7, 2023

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya kadammar da wani sabon rahoto da ke cewa an yi asarar sama da dalar Amurka bilyan 100 a yankin Arewa maso Gabashin kasar, sakamakon matsalar ta'addanci.

https://p.dw.com/p/4W5Hg
Najeriya I Arewa maso Gabas I Ta'addanci
Dubban al'umma ne suka kauracewa gidajensu, sakamakon matsalar ta'ddanciHoto: Getty Images/AFP/Stringer

Wannan rahoto da Asusun Kula da Ilimin Yara Kanana na Majalisar Dinkin Duniyar wato UNICEF ya gabatar ya yi nazari ne mai zurfi kan irin asarar dukiya, wadda ta shafi tattalin arzikin alummun jihohin yankin. Binciken na UNICEF ya gano yadda matsalar ta'addanci ta tsawon shekaru 13 ta hana yara zuwa makaranta, manya kuma suka kasa zuwa gona.

Karin Bayani: UNICEF: Harin bama-bamai da yara na karuwa

Matsalolin da UNICEF din ta ce ta gano dai, sun shafi rayuwar yara kanana sama da 9,000 da suka fuskanci mummunan cin zarafi kama daga yi musu fyade da kuma garkuwa da su a tsakanin 2017 zuwa 2021. Abin da yafi daukar hankali shi ne, yara kanana da kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai suka shigar da su ayyukan ta'adanci da yawansu ya kai sama da 5,000.

Najeriya I Arewa maso Gabas I Ta'addanci | Sansanin 'Yan Gudun Hijira na Dalori | Yara
Yara da dama na karatu a sansanonin 'yan gudun hijiraHoto: picture-alliance/dpa/Unicef/Esiebo

Asusun Kula da Ilimin Yara Kanana na Majalisar Dinkin Duniyar ya ce ko da yanzu aka kawo karshen matsalar ta'adancin, asarar da yankin za yi nan da karshen wannan shekara ta 2023 zai kai dalar Amurka bilayn 150 zuwa 200. A yayin da ake cikin wannan hali asusun na UNICEF ya daga dan yatsa a kan milyoyin yara kanan da ke fama da matsalar tamowa saboda karancin abinci mai gina jiki, ba ya ga yaran da ba su kai shekaru biyar ba da ke fuskantar karancin abincin.

Karin Bayani: UNICEF: Yara na fama da cututtuka da talauci

Christian Munduate ita ce wakiliyar UNICEF din a Najeriya, kuma ta ce lokaci ya yi da ya kamata a dauki mataki. Duk da samun saukin lamarin da gwamnati ke bayyanawa akwai sauran aiki a kan batun rashin tsaro a wannan yanki na Arewa maso Gabashin Najeriya, domin ko da a 2021 kadai mutane miliyan 200 da dubu 600 ne suka rasa muhallansu.