1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

UNICEF: Yara na fama da cututtuka da talauci

Yusuf Ibrahim JargabaJune 28, 2016

A rahotanta na shekara-shekara, hukumar mai kula yara ta ce, yara 'yan kasa da shekara 5 kusan milliyan 69 ne za su iya mutuwa a sakamakon cututtukan da za'a iya magancewa

https://p.dw.com/p/1JF82
Uganda Kinder und Mädchen mit Baby
Hoto: DW/H. Jeppesen

Kazalika wasu yaran milliyan 167 za su zauna cikin talauci yayin da kuma za´a yi wa yara yammata aure tun suna kanana kusan milliyan 750 saboda iyayensu na cikin talauci nan da shekara ta 2030 matsayin ba´a dauki matakin magance matsalolinba.

Ita dai wannan hukuma ta UNICEF ta kan fidda rahotanta ne duk shekara don bayyana halin da kananan yara ke ciki da kuma wanda za su iya shiga nan gaba, a kasashen fadin duniya baki daya.

Wannan rahoto dai ya nuna cewa akalla akwai yara kanana kusan milliyan 60 da basa zuwa makaranta a fadin duniya sannan akwai yara milliyan 250 da ke cikin kangi sakamakon fitintunu da suke faruwa a yankunansu. Ya kuma bayyana cewa akwai kuma milliyan 30 da a halin yanzu suke gudun hijira.

Pakistan Islamabad Kinderarbeit Armut
Hoto: DW/I. Jabeen

UNICEF ta yi nuni da cewar yawancin yaran da ke mutuwa a duniya sakamakon cututtukan da za´a iya magancewa kashi 80 cikin 100 ana samunsune a kudancin Nahiyar Asiya da kuma kasashen kudu da sahara na Afrika wanda rabinsu 'yan kasashen Indiya ne da Najeriya da Pakistan da Kwango da kuma Habasha.

Rahotan ya cigaba da cewa a shekara ta 2015 yara milliyan shidda ne suka rasa rayukansu kuma mafi yawancinsu a kasashen Afrika ta Yamma da kuma Afrika da Tsakiya wanda hakan ke barazana ga makomar nahiyar.

Rahotan ya ambato Najeriya a matsayin kasar da tafi yi wa yara mata kanana aure da wuri tun suna 'yan shekaru 15 fiye da kowace kasa a Nahiyar Afrika.

Kazalika kasa da rabin yaran da ake haihuwa a Afrika ta Yamma da Tsakiyar Afrika keda rigistar haihuwa, inda ake barin sauran sakakai wanda hakan kan kaisu ga yin safararsu har ta kaisu ga shiga kangin bauta.