Najeriya: Kotun koli ta ce PDP ce ta yi nasara a Zamfara
May 24, 2019Talla
Kotun koli da ke Abuja a Najeriya ta kori karar da jam'iyar APC ta shigar bangaren gwamnatin jihar Zamfara inda ta nemi kotun da ta halarta mata zabukan fidda gwani da tace ta yi. Kotun ta tabbatar cewa ba'a yi zaben fidda gwani ba dan haka kotun ta ba da umarnin a ba jam'iyyar da ta zo ta biyu nasarar a zaben. Magoya bayan jam'iyar PDP sun nuna murnarsu bayan bayyana hukunci da hadin gwiwar Alkalai biyar suka yi na kotun kolin ciki har' da mai rikon mukamin alkalin Alkalan kasar Muhammad Tanka da kuma mai shari'a Justice Galumje Adamu. Sakamakon wannan hukuncin kotun koli yanzu an tabbatar da cewar jam'iyyar APC Jihar Zamfara bangaren gwamnati da na Senator Kabir Garba Marafa sun tashi a tutar babu.