Najeriya: APC na kokarin dinke baraka
November 26, 2018Sakamakon matsaloli da suka kunno kai a Jam’iyyar APC musamman a jihohi hudu na Arewa maso Gabas guda da jam’iyyar ke mulki a cikinsu, ya sanya jam’iyyar shirya wani taro da nufin duba kalubalen da ke addabar shiyyar don lalubo hanyoyin da za’a magance su, ganin cewa yanzu ana shirin fuskantar babban zaben kasa da zai gudana a shekarar 2019 bisa la’akari da cewa jihohi biyu ne kadai a shiyyar suke karkashin jagorancin jam’iyya mai adawa ta PDP. Mustapha Salihu shugaban jam’iyyar APC shiyyar Arewa maso Gabas ya kore duk wani zargi da ake yi cewa ba a gudanar da zaben fidda gwani ba a jihar Bauchi.
Jihar Bauchi dai tana daya daga cikin jihohin Arewa maso Gabas da aka yi ta cece-kuce a kan zaben fidda gwani na jam’iyyar APC mai mulki sakamakon zargin rashin gudanar da sahihin zabe da sauran 'yan takarar gwamna a jihar suke yi ga bangaren gwamnati mai ci, lamarin da ya kai aka samu hatsaniya a sassa daban-daban na jihar da kuma rashin jituwa tsakanin shugabannin jam’iyyar, abin da jama’a ke ganin na iya tasiri ga samun nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa. To sai dai gwamnan jihar Muhammad Abdullahi Abubakar ya ce wannan batu shaci-fadi ne kawai domin su kansu a hade yake.
Shi ma a nasa bayanin, tsohon gwamnan Jihar Bauchi Malam Isah Yuguda, wanda ya dawo tafiyar jam’iyyar APC, ya bayyana cewa ko tun lokacin da ya fadi zabe a shekarar 2015 babu wata matsala tsakaninsa da gwamnan Jihar Bauchi mai ci, sabanin yadda wasu a bayan fage ke fadin wani abu daban.
Gwanonin jihohin Adamawa, Borno da Yobe sun samu halartar wannan taro wanda ya hada da sauran manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.