Mutuwar Gaddafi ta bar baya da kura
October 21, 2021Lamura sun tabarbare a kasar Libiya tun bayan kashe Shugaba Moammar Gaddafi shekaru goman da suka gabata, inda galibin 'yan kasar ke ganin cewar jiya ta fiye musu kyau, yayin da a waje guda kuma 'yan siyasa da masu fafutuka ke cewa ba sa da na sani da kawo karshen mulkin Gaddafi da suka yi.
kasashe da ke kewaye Libiyan kamar Nijar da ma kasashen Afirka ta yamma da dama na fuskantar matsalolin karayar tatalin arziki da tabarbarewa tsaro sanadiyar bazuwar makamai bayan mutuwar Gaddafi. Jihar Agadez ta fi dandana kudarta, inda baya ga yawaitar kungiyoyin 'yan ta'adda ga kuma kwararrar bakin haure sakamakon abin da ya faru bayan mutuwar Kanal Gadafi.
A daya hannun kuma, kasar ta Libiya ba ta fita daga dambarwar rikici ba, inda hatta zaben 'yan majalisar dokoki da na shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a watan Disamba aka dage shi har sai abin da hali ya yi.