1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Mexico: Rufin coci ya rufta kan masu ibada

Abdullahi Tanko Bala
October 2, 2023

Rahotanni daga arewa maso yammacin Mexico na cewa akalla mutane tara sun rasu wasu 40 kuma sun jikkata bayan da rufin coci ya fado musu yayin da suke gudanar da taron ibada.

https://p.dw.com/p/4X26E
Cocin da rufinsa ya rufta a Mexico
Cocin da rufinsa ya rufta a MexicoHoto: Alejando de Angel/El Sol de Tampico/AP/picture alliance

Lamarin ya faru ne a Santa Cruz na kasar Mexico kuma ana ci gaba da kokarin gano dalilin faduwar rufin.

Tun da farko kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito hukumomi na cewa mutane bakwai ne suka rasu yayin da aka ceto mutane goma.

Kafofin yada labaran cikin gida sun ce har yanzu akwai akalla mutane kimanin 20 da ke makale a cikin baraguzai