Har yanzu da sauran mutun 147 a karkashin baraguzai
June 30, 2021Talla
Masu aiyukan ceto na ci gaba da zakular barguzan ginin benin nan na Champlain Towers da ya ruguje a birnin Falorida na Amirka, da zimmar ganin karin wadanda ke da sauran nunfashi mako daya bayan aukuwar ibtila'in. Ya zuwa yanzu dai alkaluman wadanda suka gamu da ajalinsu sun kai 16, bayan an kara gano wasu gawarwakin mutane hudu a yau din nan, a yayin da hukumomi ke ke cewa har yanzu ana ci gaba da binciken sauran mutane 147 da suka makale a baraguzan ginin mai hawa 12. Ana sa ran a wannan Alhamis shugaban Amirka Joe Biden zai kai ziyara a wurin da hatsarin ya faru,a daidai lokacin da dangi da 'yan uwan wadanda lamarin ya rutsa da su ke cikin zullumi.