Mali: Jamus ta sanar da karshen ayyukan sojojinta a Mali
December 12, 2023Talla
Kasar Jamus ta sanar da ficewar sojojinta daga shirin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da aka fi sani da MINUSMA, a kasar Mali, kamar yadda shugabannin mulkin sojin Bamako suka bukaci hakan daga hukumomin Berlin.
Tuni dai tawagar karshe ta dakarun Jamus akalla 142 suka bar sansaninsu da ke birnin Gao dake arewa maso gabashin kasar ta Mali, a wata sanar wa da ma'aikatar tsaron Jamus ta fitar.
Sanarwar ta kara da cewa ragowar sojojin Jamus 4 da suka rage a birnin Bamako za su fice daga kasar, zuwa ranar lahadi 17 ga watan disambar 2023.