Jamus da Faransa sun gargaɗi 'yan ƙasashensu a Mali
April 2, 2012Ministan harkokin wajen Faransa Alain Juppe ya ce halin da ake ciki a Mali yana ƙara taɓarɓarewa sai dai ya ce Faransa ba za ta tura dakarunta zuwa ƙasar da ta taɓa yi wa mulki mallaka ba. Juppe wanda ke birnin Dakar yanzu don halartar bikin rantsar da sabon shugaban Senegal Macky Sall, da aka yi a wannan Litinin, ya faɗa wa manema labarai cewa ana cikin wani hali mai hatsri a Mali saboda haka ya gargaɗi dukkan Faransawa da kasancewar a Mali ba ta da wani muhimmanci da su fice daga ƙasar. Ya ce Faransa za ta iya taimakawa da kayan aiki ko ba da horo ga sojojin Mali amma ba ta girke dakarunta ba, musamman kasancewa ana garkuwa da wasu Faransawa shida a yankin, rayuwarsu ka iya faɗawa cikin wani hatsari. Shi ma ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle a cikin wata sanarwa ya yi kira ga sojoji a Mali da su gaggauta maido da mulkin doka tare da kawo ƙarshen faɗan da ake yi a arewacin ƙasar ta Mali. Wani kakakin ma'aikatar wajen Jamus ya ce gwamnatin ƙasar na kira ga dukkan Jamusawa da su guji zuwa Mali kana waɗanda ke cikin ƙasar kuma su yi ƙoƙarin ficewa. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin Yammacin Afirka su fara wani taro a birnin Dakar na ƙasar Senegal, inda suke tattaunawa akan halin da ake ciki a Mali.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas