China na amfani da maganin gargajiya a kan Covid-19
April 17, 2020Talla
Wannan dabi'a tafi samun karbuwa a kasar Indiya da China masu yawan jama'a kuma da suka kwashe shekaru masu yawa suna amfani da maganin gargajiya.
Sai dai ana samun mabanbantan ra'ayoyi. A Indiya gwamnati na shan suka bayan da ta sanar da cewa akwai wani maganin gargajiya da ka iya kare mutum daga Coronavirus. A kasar China inda cutar ta fara bulla, hukumomi sun ce maganin gargajiya na aiki sosai wurin tunkarar cutar. A kasar Venezuela kuma shugaba Nicolas Maduro ya bayar da fatawar shan wani shayi na gargajiya zai iya kawo sauki ga cutar Coronavirus.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, dai ta yi gargadi sosai a kan amfani da irin wadannan magunguna. Sai dai ta ce akwai yiwuwar maganin gargajiyar ya rage radadin cutar amma ba warkarwa ba.