Martanin taya murna ga zababben shugaban Brazil
October 31, 2022Shugabannin Jamus da Spain da Birtaniya da Rasha da Chaina na sahun farko na shugabannin duniya da suka taya zababben shugaban na Brazil Luiz Inácio Lula Da Silva murna. Galibin kasashen, sun rika fitar da sakonnin taya murnar hade da fannonin da suke sa ran yin aiki tare da Shugaba Lula da Silva wanda da kyar da jibin goshi ya samu nasara a kan shugaba mai ci Jair Bolsonaro.
Lula da Silva dai ya lula nasara a zagaye na biyu na zaben da kaso 50.9 ckin 100 na kuru'un da aka kada, a yayin da Bolsonaro ya samu kaso 49.1 na kuru'un. Bayan da kotun kolin kasar ta tabbatar da wannan nasara ga Lula da Silva dai, ya yi jawabi yana mai cewa wajibi ne jama'a su daina shan wahala.
"A yanzu wajibi ne mutanen kasar nan su fita daga cikin kunci. Wannan yanayi bai dace da mutane masu kima da soyayya da raha kamar ku ba, gwamnatin 'yan gurguzu ce ta mayar da ku haka, gwamnatin da ba ta kaunar ganin bakar fata da kuma mutanen Indiya.''
Zababben shugaban na Brazil dai ya jagoranci kasar har sau biyu a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2010. A 2018 an kama shi da laifin karbar cin hanci daga wani kamfani da gwamnatinsa ta bai wa kwangila, lamarin da ya sanya aka yi masa daurin watanni 18 a gidan maza.
A 2021 kuma kotun kolin kasar ta wanke shi daga tuhumar cin hanci da aka yi masa sannan aka sako shi, lamarin da ya ba shi damar tsayawa takara a bana. Ga dai abin da wasu 'yan kasar ke cewa a game da sakamakon zaben:
A cike nake da farin ciki domin yanzu mun zabar wa kanmu shekaru hudu na adalci da kwanciyar hankali sabanin wanda muka kayar da ya kasance shugaba tamkar dan daba ba ruwansa da abin da ya shafi sauran jama'a.
Fatana shi ne ya kawar da yunwa daga kasar nan, abinci ya yawaita a ko'ina, a kuma samu ci-gaban tattalin arziki sannan a rage yawaitar bindigogi a hannun mutane.''
A yanzu dai kallo ya koma ga bangaren shugaba mai barin gado Jair Bolsonaro wanda tun kafin sanar da sakamkon yake zargin an shirya tabka magudi ta hanyar samar da na'urorin gudanar da zaben masu tangarda. Shi kansa zababben shugaban na Brazil Lula da Silva bai fitar da tsammanin Bolsonaro zai yi watsi da sakamakon zaben ba, inda a jawabin da ya yi ga magaoya bayansa yake cewa:
Ya kamata ace tuntuni shugaban da muka kayar a zabe ya kira ni ya amince da shan kaye. Amma har zuwa yanzu bai kira ni ba. Ban sani ba watakila ya kira ni, ba ni kuma da tabbaci ko zai amince da sakamakon zaben.''
Bolsonaro mai tsattsauran ra'ayi dai, ya fara samun tirjiya daga 'yan kasar tun a shekara ta 2020 lokacin da ya yi ta musanta wanzuwar cutar corona, lamarin da ya bai wa cutar damar halaka mutanen kasar. Baya ga haka, masu adawa da shi na siffanta gwamnatinsa a matsayin mai nuna kyama ga bakaken fata. Koma dai mene ne, a yanzu Brazil ta yi sabon shugaba Lula Da Silva wanda za a rantsar wa'adi na uku a ranar daya ga watan Janairun shekara mai zuwa ta 2023.