Adadin fetur da Libiya ke hakowa ya ragu
March 13, 2020Talla
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ya ce tun daga ranar 8 ga wannan wata na Maris gangar danyen man fetur da kasar ke samarwa ta koma 114,331. A farkon shekarar nan dai rahotanni sun ce kasar na samar da akalla ganga milyan 1.2 a kowace rana. Sai dai kamfanin man fetur din kasar ya ce yanzu ko ganga 150,000 ma ba a samu.