1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwale-kwale dauke da mutane 200 ya kife a tsakiyar Najeriya

November 30, 2024

Rahotannin da ke fitowa daga jihar Neja da ke a tsakiyar Najeriya, na cewa ya zuwa yanzu mutane 27 ne suka salwanta sakamakon wani kifewar da wani kwale-kwale ya yi a tsakiyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/4nbAC
Yadda ake kwashe gwargwaki a hadarin kwale-kwale a Najeriya
Yadda ake kwashe gwargwaki a hadarin kwale-kwale a NajeriyaHoto: AP/picture alliance

Kwale-kwalen da ya yi wannan hadari wanda ke dauke ne da fasinjoji sama da mutum 200, ya rutsa ne da 'yan kasuwa mata da masu aikin gona wadanda suka nufi kasuwar mako-mako ta Katcha.

Babu kuma wani daga cikin fasinjojin da hadarin ya rusta da su, da ke sanye da rigar kariya a lokacin hadarin ruwa, abun kuma da ke nuna fargaba kan yiwuwar samun yawan wadanda za su iya rasa rayukansu.

Galibin mutanen dai sun fito ne daga Missa da ke a tsakiyar jihar Kogi mai makwabtaka da Neja, kamar yadda hukumomin agaji suka tabbatar.

Haduran jiragen ruwa dai ba sabon al'amari ba ne a Najeriya, inda a kullum ake dangantawa da gangancin daukar mutane da kaya fiye da kima.

Ko a cikin watan Oktoba ma dai an samu kwatankwacin hadarin nan a kwale-kwale a rafin Muwo Gbajibo da ke cikin karamar hukumar Mokwa na jihar ta Neja, inda mutane da dama suka rasu.