SiyasaAfirka
Jirgin ruwan kwakwale ya kife a Najeriya
October 30, 2023Talla
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta tabbatar da mutuwar mutane kusan 20 sakamakon kifewar Kwalekwale a Jihar Taraba da ke Arewacin kasar, inda wasu 14 suka jikkata, yayin da ake ci gaba da laluben sauran fasinjoji 73 da har yanzu ba a gano su a cikin ruwan ba.
Shugaban sashen kula da ayyuka na hukumar Ladan Ayuba ne ya sanar da hakan yau Litinin, yana mai cewar masunta na ci gaba da zabarin sauran wadanda suka nutse a cikin ruwan don zakulo su.
Kwalekwalen mai dauke da fasinjoji sama da 100, ya kwaso su ne bayan sun kammala cin kasuwar kifi ta Ardo-Kola da yammacin Asabar din da ta gabata.