1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama tsohon firaiministan Malaysia da cin hanci

July 28, 2020

Wata kotu a Malaysia ta samu tsohon firaiministan kasar Najib Razak da laifin almundahana da dukiyar kasa

https://p.dw.com/p/3g1Iy
Malaysia Najib Razak vor Gericht in Kuala Lumpur
Hoto: Reuters/Lim Huey Teng

Hukuncin da alkali Mohamad Nazlan Ghazali ya kwashe sa'oi biyu yana karantawa a safiyar Talatar nan ya ce tsohon firaiministan ya karkatar da dubban miliyoyin daloli da sunan shirin zuba jari a kasar a lokacin da yake kan karagar mulki. 

Tuni tsohon firaiministan ya sha alwashin daukaka kara, yana mai cewa zai bi hakkinsa har sai ya ga abin da ya ture wa buzu nadi.

Wannan zargin ne dai ya harzuka mutanen Malaysia suka kayar da gwamnatin Najib Razak a zaben shekara ta 2018. Kazalika bayan wannan shari'a tsohon firaiministan yana fuskantar wasu tuhume-tuhume a wasu kotuna a kan yadda ya gudanar da gwamnatinsa, idan kuma har ta tabbata to zai iya fuskantar dauri a gidan yari.