HdM: Matashiya mai sana'ar kwalliya
March 18, 2020Talla
Wannan matashiyar Budurwa yar Jami'an me suna Makiya Rabi'u Nabature da ke garin funtua a jihar Katsina ta shaida wa DW makasudun rungumar sana'ar
Matashiya Makiya Nabature ta ce ta sami nasarori matuka gaya da wannan sana'ar.
Hasali ma ta ce duk da kalubalen da ta ke fuskanta ta sami fadada sana'ar inda ta ke yi har a gida.
Ta ja hankalin yan uwanta mata dasu kama sana'i'o musamman dalibai saboda mahimmacin da sana'a ta ke da shi.
Mafi yawancin Dalibai sun dogara ga iyaye ko dangi wajen daukar nauyin karatunsu sai dai Makiya ta banbanta kuma ta na tafiyar da karatunta cikin nasara