1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rarrabuwar kawuna a kasar Libiya

February 17, 2021

Ana bukukuwan cika shekaru 10 da juyin juya hali a Libiya da ya kawo karshen mulkin Moammar Gadhafi. An gudanar da bukukuwan murnar a yammacin kasar. Sai dai ana ganin tamkar gwamma jiya da yau.

https://p.dw.com/p/3pUQ2
Libyen Demo zum Jahrestag der libyschen Revolution
Wasu daga cikin 'yan Libiya sun yi murnar zagayowar ranar juyin juya haliHoto: Mahmud Turkia/AFP/Getty Images

Shagulgula a yankin gabashin Libiya dangane da cika shekaru goma da hambarar da gwamnatin marigayi Shugaba Moammar Gadhafi ba su karbu ba, akasin yadda ake gani a bangaren yammacin kasar ta Libiya. Ko a yankin Benghazi da aka fara gangamin yujin juya halin a shekaru 10 da suka gabatan ma dai, babu wata sabgar da ta kama da gangamin nuna farin ciki da wannan rana.

Hukumomin kasar sun ayyana wannan Laraba (17.02.2021) a matsayin ranar hutu, ba tare da sun sanar da shirya wani gangami na musamman mai kama da biki na farin ciki ba. Wasu da dama daga cikin ‘yan kasar na cewa rashin hankali ne su gudanar da biki kan wannan lamari, saboda yadda suka dauki juyin juya halin daga bisani, a matsayin sanadi na bala’I da kasar ra Libiya ta sami kanta a ciki.

Libyen Demo zum Jahrestag der libyschen Revolution
Wasu 'yan Libiya sun yi tir da shisshigin Turkiyya a harkokinsu na cikin gidaHoto: Abdullah Doma/AFP/Getty Images

Libiya ta jima tana ganin illar shiga tsakanin da manyan kasashen duniya ke yi a cikin ta, kuma a yanzu kalubalen shi ne a samu a yi tir da irin abubuwan da ke wakana na ba daidai ba. Babban zullumin kamar yadda wasu 'yan kasar da masu nazari ke fadi, shi ne kafa kansu da kasashen Rasha da Turkiyya suka yi cikin harkokin kasar. Kasashen da ake ganin ba za su iya barin Libiyar wai kawai daga magana ta fatar baki da Majalisar Dinkin Duniya ke yi musu ba.

Wani mazaunin yankin Sabha, Hasam Mohammed, ya ce hankali ba zai kama ba a ce ana murna a Libiya ganin halin da aka samu kai a ciki.

Ya ce "Abin kunya ne a ce Libiya ta zama kasar da ta rasa kimar da aka san ta da ita, duk da irin tagomashin da take da shi a baya musamman a bagnaren ci gaba a Afirka. Yanzu mu ne muka zama masu neman yadda za mu ceto kan mu. Kokarin kowa wai yanzu shi ne yadda za a samu zabe, ko ma a samu wanda za a iya goyon bayan sa a ba shi kuri’a. kawai fatanmu shi ne samun wanda zai dawo da wannan kasar bisa martabarta da ta rasa. Babban abin so kuma a maida hankali a kai, ba zai wuce da farko manyan kasashen nan na duniya karkahsin Majalisar Dinkin Duniya, su fidda hannunsu daga al’amuranmu ba.

To amma ga mutane irin su Tarek Megerisi, na majalisar Turai mai kuma sharhi kan harkokin kasar ta Libiya, har yanzu juyin juya halin na a matsayin dama ga Libiyawa ta samun shirya gwamnatin da suke muradi. 

Tarek Megerisi
Juyin juya hali na a matsayin dama ta samun gwamnatin da ake muradi, in ji Tarek MegerisiHoto: ECFR

Ya ce ''A karon farko cikin shekaru 50 mutanen kasar Libiya sun sami damar tsoma bakinsu cikin al'amurran da suka jibanci kasarsu. Ba zan ce nasarar da aka samu ta wadatar ba, amma dai samun 'yanci da jama'a suka yi da kuma fatan da ake yi na tunanin wannan ya kawo karshen salon mulkin Gadhafi, wani abu ne musamman yadda ake da fatan cewa abubuwa za su ci gaba da sauyawa, wannan babbar riba ce da aka samu daga juyin juya halin.''

A jajibirin wannan rana ta cikar Libiya shekaru 10 da kawo karshen mulkin marigayi Shugaba Gadhafi dai, manyan birane irin su Tarabulus, sun kasance da tutocin soji, da kuma wasu da suka kwatanta wasa da tartsatsin wuta, duk da kasancewar hukumomi sun kafa dokoki na yaki da cutar corona da ke kin haduwar mutane a waje.