1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Jirgin dakon kayan DHL ya yi hatsari a Lithuania

November 25, 2024

Mutum daya ya rasu sakamakon hatsarin jirgin da ya auku da safiyar Litinin baya ga wasu biyu da suka samu raunuka.

https://p.dw.com/p/4nNw3
Wurin da jirgin dakon kaya na DHL ya fadi a Lithuania
Wurin da jirgin dakon kaya na DHL ya fadi a LithuaniaHoto: Petras Malukas/AFP

Wani jirgin dakon kaya mallakin kamfanin DHL mai aika sakonni ya yi hatsari da safiyar Litinin a kusa da filin jirage na birnin Vilnius da ke kasar Lithuania.

'Yansanda da kuma masu aikin kwana-kwana sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mutum daya ya rasu sannan biyu sun jikkata sakamakon faduwar jirgin.

Jirgin wanda kamfanin Swift Airline ke kula da shi a madadin DHL ya taso ne daga birnin Leipzig na Jamus kuma ya fadi a kan wani gida kamar yadda mai magana da yawun Hukumar Kare Bala'o'i ta kasar ya bayyana.

Hatsarin jirgin sama ya kashe sojojin Malaysia 10

Har ila yau, jami'in ya kara da cewa babu wanda ya rasu daga cikin mutanen gidan da jirgin ya rikito kansu sai dai kawai asalin fasinjojin jirgin saman mai dauke da kaya.

Masu aikin kwana-kwana sun yi ta kokarin kashe wutar da ta tashi sannan hayaki na tashi a wani gida mai nisan kilomita 1.3 da filin jirgin babban birnin kasar.

Babu wanda ya tsira da rai a hatsarin jirgin sama a Brazil

Motar daukar marasa lafiya ta 'yansanda ma ta isa wurin da gaggawa sannan an rufe tituna da dama sakamakon hadarin jirgin dakon kayan na kamfanin DHL.