Hatsarin jirgin sama ya kashe sojojin Malaysia 10
April 23, 2024Jiragen yakin kasar Malaysia masu saukar ungulu guda biyu sun yi karo da juna da safiyar Talatar nan, yayin atisaye a sararin samaniya, lamarin da ya janyo mutuwar dukkan sojoji 10 da ke cikin jiragen.
Karin bayani:Kotu ta sami Najib Razak da Almundahana
Wani babban kwamandan rundunar sojin kasar da ke aiki a sashen kashe gobara da bada agaji Suhaimy Mohamed Suhail, ya ce likitoci ne suka tabbatar da mutuwar dakarun jim kadan bayan hatsarin, kuma an garzaya da gawarwakinsu zuwa asibiti don tantance su.
Karin bayani:An harbo wani jirgin saman fasinjan Malaysia a gabashin Ukraine
Sojojin ruwan kasar ta Malaysia wato Royal Malaysian Navy na tsaka da gudanar da gwaje-gwajen ne a sansaninsu da ke yankin Lumut na yammacin jihar Perak, lokacin da wannan mummunan hatsari na taho mu gama ya auku.