Ana gudanar da zaben 'yan majalisa a Japan
July 10, 2022Talla
An bude runfunan zaben 'yan majalisa a fadin kasar Japan a wannan Lahadi. Ana sa ran zaben zai kara wa jam'iyyar tsohon Firaminista Abe goyon baya, bayan kisan gillar da aka yi masa a wajen yakin neman zabe na jam'iyyarsa ta LDP don nema wa 'yan takara a jam'iyyarsa tagomashi.
Idan har jam'iyyar ta LDP ta yi nasara kamar yadda ake hasashe, Kishida zai samu damar ci gaba da zama firaministan Japan har nan da shekaru uku ba tare da an sake komawa zabe ba.