1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta tallafa wa kananan yan kasuwa

April 1, 2020

Gwamnatin Jamus a wannan Laraba ta sanar da kebe zunzurutun kudi Euro bilyan biyu domin rage wa kananan masana'antu radadin annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3aJEO
Berlin | SPD-Bundesparteitag - Olaf Scholz
Ministan Kudin Jamus Olaf Scholz a tsakiyar wasu 'yan jam'iyyarsu ta SPDHoto: Getty Images/AFP/T. Schwarz

Ministan kudin Jamus Olaf Scholz ya sanar a birnin Berlin cewa suna fatar tallafin zai karfafa wa masu kananan sana'o'i gwiwa su fito su ci gaba da kasuwancinsu a lokacin wannan zaman-tararrabi na Corona da duniya ke ciki. 

Akalla Euro bilyan 10 ne dai gwamnatin Jamus ta kebe tun da farko don tayar da komadar tattalin arzikin kasar biyo bayan yadda Corona ke ci gaba da ragargaza tattalin arzkin duniya.

Ministan Tattalin Arziki na Jamus Peter Altmaier ya ce a 'yan shekarun nan kananan masana'antu a Jamus sun sami bunkasa dalilin ke nan da ya sa yanzu gwamnati ta fito da tallafin don kada a bar wancan ci gaba ya sulale.