SiyasaGabas ta Tsakiya
Larabawa sun sayi makamai daga hannun Jamus
January 3, 2021Talla
Kamfanin dillancin labarai na DPA ya ce kasashen da ke cikin rikicin Libya da Yemen su ne galibi suka fi sayen makaman daga hannun Jamus. Kasar Masar wace ta sayi makamai na Euro miliyan 752 ita ce ke kan gaba sai Qatar wace ta sayi makamai na Euro miliyan 305. Akwai kuma kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Kuwait da Turkiyya da su ma suka sayi makamai a hannun Jamus din. Ma'aikatar tattalin arzikin Jamus dai ta fito da wadannan bayanai ne bayan da wani dan majalisar kasar ya bukaci ta yi wa jama'a bayani dalla-dalla. Jamus din na cikin kasashe biyar na duniya da suka yi suna wurin kera makamai da sayar da su a duniya. Akwai Rasha da Amirka da Faransa da kuma China da su ma ke sayar da makaman yakin.