SiyasaJamus
Jamus ta yi kakkausar gargadi a kan corona
November 22, 2021Talla
Gargadin da ministan ya yi a wannan Litinin na zuwa ne a yayin da corona ta sanya Jamus a gaba a cikin 'yan makonnin nan, har ta kai ga duk da ingancin tsarin kiwon lafiyar kasar, asibitoci ke gargadin cewa sun fara tunbatsa da mutanen da corona ta yi wa mugun kamu.
Mutane sama da miliyan biyar cutar ta kama, a cikinsu kuma ta yi ajalin kusan mutum 100,000 tun daga farkon fara annobar a duniya.