1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kashe shugaban Hamas, Yahya Sinwar

October 17, 2024

Isra'ila ta ce ta kashe shugaban kungiyar Hamas, Yahya Sinwar a wani harin da ta kai kudancin Gaza, lamarin da ake ganin zai kawo gagarumin tarnaki ga kungiyar.

https://p.dw.com/p/4lvfS
Shugaban Kungiyar Hamas, Yahya Sinwar

Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce, Yahya Sinwar na daga cikin 'ya ta'adda uku da dakarun kasar suka kashe a farmakin da suka kai Zirin Gaza. Isra'ila dai na zargin Sinwar da kitsa kai mata hari mafi muni a tarihinta a ranar bakwai ga watan Octoban shekarar bara.

Sanarwar da Isra'ila dai na zuwa ne makwanni bayan da ta kashe shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah a wani mummunan harin da ta kai Lebanon.

Karin bayani: An yi jana'izar shugaban Hamas a Iran

Sinwar dai ya zama shugaban Hamas ne bayan da aka kashe tsohon shugaban kungiyar, Ismail Haniyeh a watan Yulin da ya gabata, kana yana daga cikin wadanda Isra'ila ke nema ruwa a jallo.