An yi jana'izar shugaban Hamas a Iran
August 1, 2024Shugaban addinin kasar Iran, Ayotollah Ali Khamenei ya jagoranci jana'izar shugaban kungiyar Hamas, Ismail Haniyeh bayan da ya gamu da ajalinsa a wani harin da ake zargin Isra'ila ta kai kan gidansa a birnin Tehran. Ana sa ran, Ayotollah Ali Khamenei ya kara jagorantar taron addu'o'in birne marigayin a birnin Doha na kasar Katar, bayan ya sha alwashin daukar fansa a kan kisan.
Karin bayani: An kashe shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Iran
Dubban mutane ne dauke da hotunan Haniyeh da kuma tutocin Falasdinu suka yi jerin gwano domin bin sallar gawar marigayin a Jami'ar Tehran. A ranar Laraba ce aka tabbatar da mutuwar Ismail Haniyeh da wani dogarinsa yayin da yake ziyara a Iran domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasar.
Karin bayani: Martanin kasashen duniya bayan kisan Ismail Haniyeh
Wasu kasashen duniya dai na ci gaba da martani kan kisan jagoran na Hamas, sai dai Isra'ila har yanzu bata ce uffan ba game da harin na birnin Tehran.