Harin bam ya kashe mutum 11 a Somaliya
August 17, 2024Talla
'Yansanda a Somalia sun bayyana cewa akalla mutum 11 ne suka rasu a wani harin ta'addanci da aka kai kan wani gidan cin abinci a ranar Asabar a birnin Mogadishu.
'Yansandan sun kuma ce wani bam ne da aka tayar daga nesa ya kashe mutanen wadanda akasarinsu fararen hula ne tare da raunata wasu mutum hudu.
Gidan cin abincin ya yi suna wajen tara jami'an tsaro a cewar 'yansandan kuma tuni Kungiyar al-Shabbab ta dauki alhakin wannan sabon harin.
Wani harim bom ya haddasa mutuwa a Somaliya
A baya-bayan nan Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi ma'aikatanta game da yiwuwar iya fuskantar hare-haren 'yan ta'adda a Somaliya, inda ta bukace su su guji shiga wuraren taron jama'a da kuma ofisoshin gwamnati.