Somaliya: Al Shabaab ta kai hari kan sansanin soji
March 23, 2024Wani jami'in sojin kasar da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, maharan sun kai harin kunar bakin wake ne da motoci dauke da bama-bamai a sansanin Sojin Busley da ke yankin Shabelle a Kudu maso yammacin kasar. Jami'in ya ce, an samu nasarar fatattakar mayakan bayan da suka yi yunkurin kwace iko da sansanin.
Karin bayani: Al Shabaab ta kashe sojojin Somaliya 61
Jami'in ya kara da cewa, dakarun soji 7 ciki har da kwamandan sansanin da kuma mayakan kungiyar 10 ne suka rasa rayukansu a musayar wutar da aka yi a tsakanin bangarorin biyu. Mazauna yankin sun kuma bayyana cewa, mayakan na al-Shabaab sun kona ababen hawan sojoji tare da yin awon gaba da wasu.
Sai dai a cikin sanarwar da ta fitar na daukar alhakin kai hari, kungiyar al-Shabaab ta yi ikrarin kashe dakarun gwamnati 57. Kawo yanzu dai gwamnatin Somaliya ba yi martani kan harin ba.