1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta jefa dubban 'yan Ukraine cikin mawuyacin hali

November 28, 2024

Dubban daruruwan mutane a Ukraine, sun shiga cikin mummunar yanayi a lokacin sanyi, sakamakon hare-haren da Rasha ke kai wa cibiyoyin samar da wutar lantarki.

https://p.dw.com/p/4nWin
Hoto: REUTERS

Sama da mutum miliyan guda ne a Ukraine ke rayuwa babu wutar lantarki a wannan lokaci da ake cikin matsanancin sanyi.

Wasu sabbin hare-haren Rasha a wannan Alhamis a yankuna da dama na Ukraine din da makamai masu linzami gami da jirage marasa matuka, su ne suka haddasa daukewar wutar ta lantarki.

Kasar ta Ukraine dai na cikin shirin kasancewa cikin yanayin sanyin da ba ta ga irinsa ba, cikin kusan shekaru uku na yaki tsakaninta da Rasha.

Wani babban jami'i a fadar Shugaba Volodymyr Zelenskyy, ya ce Rasha na tsananta hare-hare a musamman tashohin samar da makamashi, da nufin hana fararen hula lantarki da kuma damar amfani da na'urorin dumama gidaje.