Hama Amadou ya yi kalaman tada kura
May 23, 2019Hama Amadou ya yi kalamai kan sojojin da ake kashewa a yakin da kasar ke yi da ‘yan ta'adda, kalaman da ofishin ministan tsaron kasar ta Nijar ya ce ya saba wa dokokin kasa, inda ma ya mika batun ga hannun babban mai shigar da kara na gwamnati, domin a cewarsa kalaman ka iya katse kuzarin sojojin kasar ta Nijar a daidai lokalin da ake cikin yanayi na yaki.
Har ila yau kalaman na zuwa daidai lokacin da wasu ‘yan kasar ke fatan ganin an samu kwanciyar hankali da hadin kan juna domin fuskantar matsalar tsaron da kasa ke fuskanta. A daidai wannan lokaci ne kuma wata sabuwar guguwa ta taso wadda idan ba a yi hankali ba, za ta kara nesanta bangarorin da ba sa ga majici da juna na masu mulki da 'yan adawa. Hakan kuwa ya dauko asali ne bayan kalaman da magudun ‘yan adawar kasar Hama Amadou ya yi a kasar ta Tukiyya inda ya ce da gangan ake tura wani rukuni na sojojin na Nijar inda ake hallakasu, kalaman da ministan tsaron kasar ta Nijar Kalla Moutari ya ce ko kadan bai dace ba ga duk wani mai kishin kasar ta Nijar ya furta haka.
Tuni dai ba da wata-wata ba magoya bayan jam'iyyar Lumana Afirka ta Hama Amadou suke ta mayar da martani kan wannan batu musamman ma ta kafofin sadarwa na zumunta, inda ta nan ne aka wallafa hirar da Hama Amadou ya yi a Turkiyya. Bana Ibrahim na daya daga cikin na hannun daman madugun ‘yan adawar Hama Amadou cewa ya yi gaskiya Hama Amadou ya fada kasancewar kasar ta Nijar kowa ya sani mutane kansu ya rabu akwai bangaren masu iko da bangaren talakawa.
A kafofin sada zumunta dai masu goyon bayan madugun ‘yan adawar Hama Amadou na nuna cewa gwamnatin na nuna son rai kan wadanda take son ta zarga da laifuka, yayın da masu adawa da kalaman na Hama Amadou ke ganin cewa matakin da gwamnatin ta dauka na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro ya yi daidai.
Tuni dai wasu ke kallon kalaman na Hama Amadou a matsayin wata hanya ta tsokana ganin cewa daman yana fuskantar babban kalubale na tsayawa takara yayin da wasu ke ganin cewa ai bangaran gwamnati ne ma ke son batar da sahu, domin karkatar da mahawarar da ake yi ta kashe-kashen sojojin kasar da ma batun kundin zabe da na hukumar zaben CENI da ake ganin an kasa samun jituwa tsakanin gwamnati da ‘yan adawa.