Gwamnatocin Afirka sun tasamma yakar Ebola
August 19, 2014Mutane 1100 ne Ebola ta yi sanadinsu ya zuwa yanzu, yayin da aka kebe wasu karin 2100 domin yi musu gwaji sakamakon hasashen da ake yi cewar sun kamu da cutar. Saboda haka ne ta haddasa fargaba a kasashen Afirka da dama, inda suka dauki matakan rigakafi.
Kamfanin jiragen sama na kasar Kenya wato Kenyan Airways ga Misali, ya katse zirga-zirgansa a kasashen Laberiya da Saliyo inda Ebola ta fi kamari. Ita ma Côte d' Ivoire ta haramta wa jiragen ruwan da suka fito daga kasashen da ake fama da Ebola ratsa mashigin ruwanta. A tarayyar Najeriya kuwa, ba fasinja da ke iya shiga jirgin sama matukar ba a yi masa gwajin da ke nuna mizanin zafin jikinsa ba.
Tababa dangane da matakan kariya
Sai dai kuma tuni masana suka fara nuna tababa dangane da irin nasarori da za a samu sakamakon amfani da wadannan matakai don yakar Ebola. Dieter Häussinger, shugaban cibiyar Hirsch ta Jamus da ke nazarin cututtukan da ake samu a Afirka da yankin Latine Amirka, ya ce babu tabbacin cewar kwalliya za ta biya kudin sabulu, ma'ana Ebola ba za ta yadu a wadannan kasashen na Afirka ba.
Inda gizo ke saka dai shi ne, jami'an kasashen na Afrika ba sa iya banbanta wanda ya ke fama da zazzabi ko mura da kuma wanda ya kamu da cutar ta Ebola.
Sai dai kuma akasarin al'ummar tarayyar ta Najeriya sun fi amfani ne da motoci wajen yin tafiye-tafiye daga wannan gari i zuwa wancan. Alhali da kamar wuya gwamnati ta yi nasarar daukan matakan rigakafin Ebola a wadannan hanyoyi sakamakon yawan matafiya da kuma rashin kayan aiki.
Masana sun nunar da cewar babu wani dalilin da ke sa gwamnatocin Afirka daukan matakai fiye da kima a yunkurin da suke yi na kare kansu da Ebola. Suka ce tarin fuka ya fi saurin yaduwa tsakanin al'umma fiye da Ebola sakamakon kamuwa da ita da ake yi ta iskar da ake shaka da kuma mu'amalla da wanda ke dauke da kwayar cutar ta TB.
Mawallafa: Hilke Fischer/ Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Pinado Abdu Waba