1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashewar tankar mai ta haddasa mace-mace a Jigawa

Abdoulaye Mamane Amadou Zainab Rabo/ Mouhamadou Awal Balarabe
October 16, 2024

Mutane fiye da 140 sun mutu yayin da kusan 50 suka jikkata bayan da babbar motar dakon man fetur ta yi hatsari a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya, a daidai lokacin da ake fama da tashin farashin man fetur.

https://p.dw.com/p/4lsK1
Yadda aka yi jana'izar wadanda fashewar tankar mai ta rutsa da su a jihar Jagawa
Yadda aka yi jana'izar wadanda fashewar tankar mai ta rutsa da su a jihar JagawaHoto: Sani Maikatanga/AP/picture alliance

 

Wadanda abin ya rutsa da su na kokarin kwasar man da ya zuba a kan hanya bayan fashewar tanka da ta afku a yammacin ranar Talata a jihar Jigawa, kamar yadda mai magana da yawun ‘yan sandan, Lawan Shiisu Adam ya shaida wa 'yan jarida. Tuni  kungiyar likitocin Najeriya ta yi kira ga mambobinta da su gaggauta kai daukin gaggawa ga wadana hatsarin ya rutsa da su, a lokacin da direban motar dakon man ya yi kokarin kauce wa wata motar da ta fadi.

Karin bayani: Karancin fetur ya kunno kai a Najeriya

Mazauna garin Majiya sun gudanar da jana'izar wadanda hatsarin ya ritsa da su. Kuma ma'aikatan agajin gaggawa suka ce ba a gane yawancin gawarwakin ba saboda kuna. Jami’an bayar da agajin gaggawa sun isa wurin da fashewar tankar mai ta faru sa’o’i da dama
bayan hatsarin. Wani mazaunin garin Sani Umar ya shaida wa 'yan jarida cewar: "Gobarar ta bazu cikin sauri, lamarin da ya sa da yawa sun kasa tserewa."

Karin bayani: Najeriya: Kokarin dakile satar man fetur

Najeriya da ke zama giwar Afirka ta fannin tattalin arzikin man fetur ta fada cikin wani wadi na tsaka mai wuya, da ya kai mahukuntan Abuja cire tallafin man fetur, matakin da ya sa farashinsa ya yi tashin gwauron zabi. Sai dai kasar ta saba fuskantar fashewar tankar mai, inda a  watan Satumban 2024, wata motar dakon kaya dauke da dabobi ta yi taho mu-gama da tankar dakon man fetur tare da haddasa mutuwar mutane 59 a jihar Neja.