1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faduwar mota da ke dakon fetur ta haddasa mace-mace a Zinder

Mouhamadou Awal Balarabe
October 23, 2023

Wani jami’in ofishin gwamnan Zinder ya bayyana cewa mutane shida sun mutu yayin da wasu karin kusan talatin sun ji rauni a lokacin da suka yi kokarin kwasar ganima sakamakon fashewar tankar man fetur.

https://p.dw.com/p/4XvIV
An samu irin wannan faduwar tankar da ke dakon man fetur a kusa da Yamai a 2019
An samu irin wannan faduwar tankar da ke dakon man fetur a kusa da Yamai a 2019Hoto: DW/S. Noukari

Mutane shida sun rasa rayukansu sakamakon faduwar wata tankar dakon man fetur a kusa da wani kauye da ke yankin Zinder na Jamhuriyar Nijar. Wani jami'in ofishin gwamnan Zinder ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa wasu karin mutane kusan talatin sun ji rauni a lokacin da suka yi kokarin kwasar ganima sakamakon fashewar tankar.

Karin bayani: Nijar ta kammala shirin shiga hago man fetur ɗinta

A cewar shafin labarai na Zinder-Infos, lamarin ya afku ne a ranar Lahadi, yayin da wasu manyan motocin tanka guda biyu suka kife bayan suka yi taho mu gama a Tirmini, wani gari mai nisan kilomita 10 daga Zinder. Dama dai Zinder ne cibiyar kamfanin Soraz da ke tace man fetur na Nijar, inda ake yawan samun faduwar motocin dakon man fetur tun bayan da kasar ta fara hako wannan arziki a 2011.

Karin bayani: Nijar za ta sayar wa Najeriya man fetur 

Ko da a watan Oktoban 2022 ma dai, wasu mutane bakwai sun mutu a irin wannan yanayi a wani kauye da ke yankin Zinder, a lokacin da suka yi tururuwar zuwa diban mai daga wata motar dakon mai da ta fadi a hanyarta ta zuwa Yamai. A cikin shekaru hudun da suka gabata ma dai, mutane 76 sun mutu sannan kusan 40 suka kone kurmus a birnin Yamai, bayan da wata tanka ta fashe a kan hanyarta ta zuwa makwabciyar kasa Burkina Faso.