Nijar ta kammala shirin shiga hago man fetur ɗinta
November 18, 2011A jamhuriyar Nijar gwamnati ta bayyana farashin kuɗin man fetur da za'a hakowa a tace shi a matatar da aka kafa a birnin Damagaram. sai dai ƙungiyoyin kare yancin bil'adama da wasu al'ummar kasar sun bayyana takaicin su a game da tsadar kudin da gwamnatin ta tsauwala,
Matatar man za ta dinga tace mai ganga 20.000 a kowace rana, kuma abu uku za ta tace ta fito da shi, sune man fetur,na diesel ko gazoil,da iskar gas. Akan tsada farashin su da za'a sayar da shi kuwa, fetur zai kama CFA 579 a ko wace lita guda, sai man diesel ko gazoil 577 ko wace lita kana za a riga sayar ko wani tulun iskar gas mai nauyin kilo 12 a farashin 3700 CFA.
Wannan tsauwalallen farashin bai wa mutane mamaki ba, don an dade da jitajitar za'a sayar da shi da tsada, bayan kira da shugabannin kungiyoyin farar hulla da suka sha yi. Kafin dai ministan man Bubakar Fumakoy Gada ya bayyana farashin man a hukumance ga manema labarai. Sai da ministan ya kira shugabannin kungiyoyin farar hulla suka yi doguwar ganawa wanda suka bashi shawarar su a kan farashin. daga cikin wadanda ministan ya gana da su har da Mamman Nura, shugaban daya daga cikin kugiyoyin dake yaki da tsadar ruwa ADDC Wadata da Mamman Lawan Gayya, darektan man a ofishin ministan man.
A kowace shekara wannan farashin zai dinga sauka kasa wato nauyi zai dinga ragewa. Amma a nasu waje talakawa abin ya basu takaici da suka ji kwatsom ana sayar da man haka kamar yadda wasunsu suka bayyana wa wakilinmu Mahamman Kanta
A ranar 28 ga wannan watan Novemba ne za'a yi bikin kaddamar da fara aikin matatar, dai-dai wannan farashin fara aiki kamawan watan Disamban mai kamawa. Iskar gas za'a fara saida shi a ranar daya ga Disamban, bayan kwanaki biyu a fara saida man fetur da diesel ko gazoil
Mawallafa: Ahmadu Tijani Lawal da Mahaman Kanta
Edita: Usman Shehu Usman