SiyasaAfirka
Majalisar Faransa ta hana amfani da hijabi a wasanni
January 19, 2022Talla
Majalisar Dattawan Faransa ta kada kuri'ar amincewa da haramta amfani da hijabi a tsakanin 'yan wasa mata a gasar wasanni a fadin kasar. Matakin da suka dauka a yammacin ranar Talata ya samu amincewa daga galibin 'yan majalisar da suka fito daga jam'iyyar Les Republicains. Sabuwar dokar ta ce sanya hijabi komi kankantarsa ga 'yar wasa ka iya zamar mata hatsari ga lafiyarta a yayin atisaye.