1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Euro 2024: Faransa ta tsallaka zuwa quarterfinals

July 2, 2024

Yanzu bayan samun tsallakawa zuwa quarterfinals a 'daddafe', Faransan za ta fafata da Portugal ko Slovenia a wasan da za ta buga a ranar Litinin mai zuwa a birnin Frankfurt.

https://p.dw.com/p/4hlFc
Hoto: Marcus Brandt/dpa/picture alliance

Faransa ta tsallake zuwa matakin dab da kusa da na karshe wato quarterfinals a gasar kwallon kafa ta nahiyar Turai, Euro 2024 da ke gudana a nan Jamus. Hakan ta faru ne sakamakon sa'ar da Faransa ta samu ta doke Belgium da 1-0.

Bayan tataburtsa da kungiyoyin biyu suka yi a filin wasa na Duesseldorf, dan wasan Belgium Jan Vertonghen ya ci gida ana kusa da kammala wasa, a minti na 85, lamarin da kai tsaye ya mika nasarar wasan mai zafi ga Faransa wacce tun da aka fara gasar ta bana 'yan wasanta ba su nuna watabajinta ba.

Duk da kasancewar Kylian Mbappe, fitaccen dan wasanta mai buga wa a kulob din Real madrid, 'yan wasan Faransa sun gaza cin kwallo da kansu duk da cewa sune suka fi sarrafa kwallo a wasan nasu da Belgium na ranar Litinin da daddare.

Tun da aka fara gasar ta Euro 2024, Mbappe ne kadai dan wasan Faransa da ya zura kwallo shi ma kuma ta hanyar bugun daga kai sai mai tsraon gida na 'penalty' a wasan da Faransan ta yi da Poland wacce tuni aka cire ta a gasar mai daukar hankalia nahiyar Turai.