SiyasaJamus
Turai ta amince a fara rigakafin corona
December 21, 2020Talla
Da ma dai an tsammaci amincewar hukumar ganin yadda kasashen Turai suka sanya ta a gaba, su na jiran amincewarta kafin su fara amfani da rigakafin.
Hukumar gudanarwa ta EU ita ma ta sanar da amincewarta dangane da rigakafin ta corona, hakan kuma na nufin daga yanzu kowace kasa a nahiyar na da ikon fara amfani da ita.
Jamus dai tuni ta sanar da aniyarta ta fara rigakafin coronar daga ranar 27 ga watan Disamba. Amincewar da hukumar ta European Medicines Agency ta yi ta share fagen fara rarraba allurar rigakafin coronar da ta kai miliyan 450 a kasashen Turai domin dakile ci gaba da bazuwar cutar.