Equatorial Guinea ta rufe iyakarta da Kamaru
November 1, 2022Talla
Mataimakin shugaban kasa Teodoro Nguema Obiang Mangue bai bayyana ranar da ake sa ran sake bude iyakokin kasar da Kamaru da Gabon ba, amma ya ce za a iya ci gaba da amfani da sufurin sama wajen kulla alaka a tsakanin makwabtakan kasashen da Equatorial Guinea.
A watan Afrilun shekara mai zuwa ya kamata a gudanar da zaben shugaban kasar, to amma gwamnatin kasar mai mutane miliyan 1.3 ta dawo da shi wannan wata na Nuwamba domin gudanar da zaben lokaci guda da na 'yan majalisar dokoki domin rage kashe kudin gudanar da zabubbukan.