1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Donald Trump na nade-naden mukamai a sabuwar gwamnatisa

Abdoulaye Mamane Amadou ATB
November 12, 2024

Makwanni gabanin ya karbi rantsuwar kama aiki, zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump na ci gaba da nade-naden manyan mukamai a sabuwar gwamnatisa.

https://p.dw.com/p/4muCU
Donald Trump zababben shugaban kasar Amurka
Donald Trump zababben shugaban kasar Amurka Hoto: Julia Demaree Nikhinson/AP/dpa/picture alliance

Sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump na ci gaba da bayyana sunayen mutanen da ake ganin za su kasance mambobi a gwamnatinsa idan ya karbi rantsuwar kama aiki a farkon watan Janairu na sabuwar shekara.

Karin Bayani : Afirka na fatan samu kulawa daga Donald Trump

Jardiar New York Times ta ambato yiwuwar Shugaba Trump ya nada Sanata Marco Rubio a matsayin babban sakataren harkokin wajen kasar Amurka a karkashin mulkinsa.

Marco Rubio mai shekaru 53 na daya daga cikin 'yan takarar da suka bayyana anniyar yi rike wa Donald Trump gargada a zaben da ya lashe a matsayin mataimaki a yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar Republican.

Karin Bayani : Donald Trump ya sanar da wanda zai kori bakin haure daga Amurka

Sabon shugaban na Amurka Donald Trump ya zabi Elise Stefanik wata mai rajin kare manufofin Trump a matsayin sabuwar jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, matakin da tuni ya dadawa Isra'ila.