Trump ya sanar da mutumin zai kori bakin haure daga Amurka
November 11, 2024Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana rikakken na hannun damansan nan Tom Homan a matsayin shugaban hukumar shige da ficen iyakokin kasar, daga wasu nade-naden da shugaban ke yi a gabanin rantsar da shi kan madafan iko.
Karin Bayani : Shugabannin duniya na taya Trump murnar lashe zabe
A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta Truth Social, sabon shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba wani wanda ya fi cancanta da rike mukamin na kula da iyakokin kasar fiye da Tom Homan, wanda Donald Trump ya kira da cewa zai yi iya kokarinsa na korar duk wasu 'yan kasashen ketaren da ke zaune a kasar ba kan ka'ida ba.
Karin Bayani : Donald Trump ya ayyana lashe zaben Amurka
Daman Tom Homan ya taba rike mukamin shugaban hukumar a wa'adin Shugaba Trump na farko wanda a lokacin gwamnatinsa ta kori kusan yara dubu hudu ta hakikance ba sa da hurumin zama cikin kasar.