1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Sabbin dokokin yaki da corona

September 29, 2020

Gwamnatin Jamus a wannan Talata ta zayyana sabbin dokokin takaita yaduwar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3jBPO
Deutschland Angela Merkel bei Beratungen der Ministerpräsidenten über die Corona-Pandemie
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

Gwamnatin Jamus ta ce daga yanzu duk garin da ke da kimanin mutum 100,000 kuma aka samu mutum sama da 35 da suka kamu da corona a cikin mako daya, to za a takaita taruwar jama'a a wannan gari.

Taron majalisar zartarwa da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta jagoranta ya zartar da cewa kada taron jama'a ya wuce mutum 25 ko kuma 50 idan taro ne na al'umma a irin wadannan wurare. Kazalika hukumomi sun ce za su fara cin tarar Euro 50 ga duk mutumin da ya bayar da lambar waya ta bogi a gidan cin abinci. 

Shugabar gwamnatin ta Jamus ta nuna damuwa kan yadda ake samun karuwar masu corona a kasar, tana mai cewa idan ba a dauki mataki ba kasar za ta rika samun sabbin kamu na corona mutum 19,000 a kowace rana.