SiyasaAfirka
Babu alamun kaddamar da kudin ECO
September 27, 2020Talla
A watan Disambar bara ne dai kasashe takwas na yankin suka cimma matsayar fara amfani da takardar kudin a karshen wannan shekara.
A yayin da yake magana a ranar Asabar Mr. Ouattara ya ce yanzu kowace kasa ta mayar da hankalinta kan yadda za ta fita daga radadin coronavirus. Ya ce sharadin fara amfani da ECOn shi ne sai kasashen sun rage basukan da suke karbowa domin aiwatar da kasafin kudinsu, yana mai cewa da zuwan corona kowa ya san wannan ba mai yi wa bane a yanzu.
Sai dai shugaban na Côte d'Ivoire na magana ta kashin-kansa ne domin sauran kasashe irinsu Benin da Burkina Faso da Guinea-Bissau da Mali da Nijar da Senegal da kumaTogo ba su hadu sun tsayar da matsaya a kai ba.