Nijar:Bukatar sauya kudin CFA
January 30, 2019A baya dai mataimakin shugaban gwamnatin kasar Italiya ne ya farfado da wannan batu na kudin CFA, inda ya ce wannan kudi na kasashen Afirka renon Faransa, ya kansance wani babban kalubale ga tattalin arzikin Afirka. Ministan kudin na Nijar Hassoumi Massaoudou dai ya jinjina wa kudin na CFA, inda ya ce yana taimaka wa wajan samun kwanciyar hankali a fuskar saye da sayarwa, sannan alakarsa da kudin Euro wannan ba wani sabon abu ne ba domin abin da yake da mahimmanci ita ce siyasar kudin da aka samar da za ta ba da damar bunkasa tattalin arziki da kuma ci gaba nan zuwa wani lokaci.
Shugaban Nijar ya taba tattauna batun na canza kudin CFA da tsohon shugaban kasar Benin
Sai dai duk da wannan tsokaci da ministan na kudi na Nijar ya yi na cewa bai ga laifi ga kudaden na CFA ba, ta shafinsa na Facebook, ofishin minista mai magana da yawun gwamnatin na Jamhuriyar Nijar ya shaida cewar shugaban kasa Issoufou Mahamdou ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasar Bernin Nicephore Soglo, wanda shi ma ya tabbatar da mahimmancin samun kudin na bai daya da kasashen ke yunkurin yi nan zuwa wani dan lokaci.