1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Binciken Boko Haram ya dagule a Nijar

Abdoullaye Mammane Amadou June 12, 2015

Wannan bincike ya dauki sabon salo bayan da daya daga cikin masaraunatan gargajiya da aka tsare bisa tuhumar alaka da Boko Haram ya ce ga garunku nan a hannun 'yan sanda a Nijar.

https://p.dw.com/p/1FgTy
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Shugaba Mahamadou Issoufou na NijarHoto: F. Batiche/AFP/Getty Images

Dan shekaru akalla 47 Malam Bulama Madayi na shugabancin wani kauye ne mai suna Dagaya da ke yankin Diffa kana ya shiga hannun jami'an 'yan sanda ne tun a farko farkon watan Mayu sakamakon zarginsa da hukumomin kasar ke yi na cewar yana kin bayar da cikakken hadin kai wajan zakulowa da bincike a yakin da kasar ta ke yi da mayakan Boko Haram a yankin na Diffa.

Bayan shafe dan lokaci a hannu 'yan sanda daga bisani hukumomi sun garzaya da shi izuwa gidan kason Kollo tare da sauran 'yan uwansa bakwai da daukacinsu hakimai ne da hukuma ke zarginsu da rashin bayar da cikakken hadin kai a yaki da 'yan Boko Haram, inda daga can ne Mariganyin ya kamu da wata rashin lafiya kana kuma bayan gabatar da shi a asibiti ya ce ga garinku nan.

Alamun tambaya cikin bayanan jami'an gwamnati

A wani taron manema labarai da lauyoyin hakiman suka kira, lauyoyin sun nuna rashin cikakkiyar gamsuwa ga bayanan farko da hukumomin kasar suka gabatar musu. Rabiou Mahamane Oumarou na daya daga cikin lauyoyin Hakiman:

Boko Haram Kamerun Nigeria Grenze
Jami'an tsaro a kan iyakaHoto: PATRICK FORT/AFP/Getty Images

"Muna so a tabbatar mana da hakikanin gaskiya a hukumance da likitance menene hakikanin abinda ya kashe hakimin nan, muna jiran wannan idan wannan takardar ta fito tun da likita ne rantsatstse zai yi aikin kuma zai yi bincike kuma shi zai fadi, Wannan ne kawai zai gamsar da mu"

Tun daga farko dai lauyoyin marigayin sun koka da rashin tuntubar 'yan uwansa da aminan arzika da ma su lauyoyin, domin samun cikaken labarin rashin lafiyarsa, kafin daga bisani a garzaya da shi babban asibitin da Allah ya yi masa cikawa kamar yadda Mahamane Oumarou ke cewa:

"Ya kamata a ce tun da rashin lafiyarshi ta samu a shedawa 'yan uwansa da aminan arziki a sanar da mu don daukar mataki, 'yan uwanshi su zo su yi jinya. Mun yi nadamar abin da ya sa ba'a sanar damu ba, tunda da muka bincika a gidan yarin Kollo kawai yakai kwanakki shidda baya da lafiya, to yanzu muna jira a bamu daukacin takardun da ke kumshe da cikakken bayani na lafiyarshi mu bincika mu gani" .