1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Wasu dalilai suka janyo yunkurin juyin mulkin?

May 21, 2024

Kwanaki bayan ikrarin dakile yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, har yanzu masharhanta na ci gaba da sa ayar tambaya kan yadda maharan suka yi wa fadar shugaban kasar kutse.

https://p.dw.com/p/4g6mZ
Bayan yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Kinshasa
Bayan yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Christian Malanga/Handout/REUTERS

,

Da misalin karfe hudu na tsakaliyar daren ranar Lahadin da ta gabata wasu bayanan farko suka fara nuni da cewa akwai rade-radin boren sojoji a unguwar manyan ma'aikata ta Gombe da ke birnin Kinshasa. Jami'ain tsaro kimanin 40 ne aka hakikance sun fantsama a unguwar da ke kumshe jakadodin kasashen ketare da manyan hukumomin gwamnatin kwango, uwa uba ofishin ministan kudi da tattalin arziki Vital Kamerhe.

Karin Bayani: Tshisekedi na yunkurin karfafa hulda da kasashen duniya

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Bayan yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Samy Ntumba Shambuyi/AP Photo/picture alliance

Bataliyar sojojin da ta kai harin ta shafe tsawon lokaci tana barin wuta da manyan bindigogi, kafin sojojin da ke yi wa gwamnati biyayya su murkushe su. Daga bisani sojin sun kuma rakaya zuwa fadar shugaban kasa Félix Tshisekedi, duk da yake rahotanni sun ce sojojin ba su tarki sa'a ba domin kuwa a fadar ba Shugaba Tshisekedi a wannan lokaci, hasalima dakarun da ke gadin fadar sa sun musu lale da barin wuta, sun tsarwatsa maharan sun kuma kama wasu daga ciki. Gwamnatin kasar ta sanar da cewa ta dakile yunkurin juyin mulki, ta kuma bayyana kwakwaran hujjojin da ke cewa akwai wasu sojojin haya daga ketare.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Bayan yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Arsene Mpiana/AFP

Duk da dumbin tambayoyin da masharhanta ke yi wa batun na yunkurin kifar da gwamnatin Kwango, wasu manyan hukumomin kasashen ketare sun bayyana rashin jin dadi da yanayin da kasar ta so ta shiga, ciki har da shugaban hukumar gudanarwa na kungiyar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat da ya yi Allah wadarai da yunkrin na juyin mulki a Kwango, tare da jinjina wa zaratan sojojin da ke kare gwamnatin kasar da suka murkushe masu da'awar karbar mulkin da tsinin bundiga.