Kwango: Tshisekedi ya nada sabuwar Firaiminista
April 1, 2024Watanni uku bayan zaben Jamhuriyar Dimokuradiyya Kwango, shugaba Felix Tshisekedi ya nada Judith Suminwa Tuluka a matsayin sabuwar Firaiminista kamar yadda gidan talabijin din kasar ya ruwaito a ranar Litinin 01.04.2024 a cikin wata sanarwa da ta fito daga fadar gwamnati.
Judith Suminwa Tuluka da a baya ke rike da matsayin ministar tsare-tsare na zama mace ta farko da ke darewa kan wannan mukami a kasar da Gabashin Afrika.
Nadin na matar mai shekaru kusan 50 a duniya wace ta gaji tsohon Firaiminista Jean-Michel Sama Lukonde wanda ya yi murabus daga mukaminsa a ranar 21 ga watan Fabarairun da ya gabata na zuwa ne watanni uku bayan zaben kasar da aka gudanar a watan Disamban bara wandan ya bai wa shugaba Tshisekedi wa'adin mulki a karo na biyu bayan ya yi nasara da gagarumin rinjaye.