AU ta dakatar da Gabon daga ayyukanta
August 31, 2023Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran rantsar da Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban gwamnatin soji ta rikon kwarya. A cewar jagororin da suka yi juyin mulki a kasar, Oligui zai jagoranci Gabon nan da zuwa wani lokaci, ko da yake ba su bayyana tsawon lokacin da za su rike madafun ikon kasar ba kafin mayar da ita kan tafarkin dimokradiyya.
Karin bayani: Sharhi: Nazari a game da yunkurin juyin mulkin Gabon
Kakakin kwamittion rikon kwarya, Ulrich Manfoumbi Manfoumbi ya bukaci dukannin sakatarori da ministoci da daractoci da sauran jami'an gwamnati da su koma bakin tare da ci gaba da gudanar da ayyukan jama'a.
Ya kuma kara da cewa, Janar Oligui ya na mai tabbatarwa dukannin abokan huldar kasar cewa, zai dauki dukkanin matakin da ya kamata wajen kare mutuncin kasar a cikin gida da kuma ketare.