1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban kasar Guinea Bissau ya bayyana yunkurin juyin mulki

December 3, 2023

Shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo, ya bayyana harbe-harben bindiga da aka ji a babban birnin kasar, da wani yunkuri ne na juyin mulki da nufin gurguntar da tsarin mulkin dimukuradiyya da kasar ke a kai.

https://p.dw.com/p/4ZjGh
Hoto: João Carlos/DW

Shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo, ya bayyana harbe-harben bindiga da aka ji a babban birnin kasar a ranar Juma'ar da ta gabata, da wani yunkuri ne na juyin mulki da nufin gurguntar da tsarin mulkin dimukuradiyya da kasar ke a kai.

Harbe-harben ya biyo sakin wasu ministocin kasar biyu da aka yi ba bisa kaida ba, wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa da wasu rukuni na masu tsaron fadar shugaban kasar suka bude wuta,

Shugaba Umaro Sissoco Embalo ya ce tuni ya dauki matakin ladabtar da shugaban rundunar tsaron fadar shugaban kasa Victor Tchongo, da ke da hannu a yunkurin na juyin mulki, abin da ya ce cin amana ce karara, kamar yadda ya shaida wa mahalarta majalisar tsaron kasar.

Jim kadan da dawowa daga halartar taron COP28 a Dubai, Embalo ya ce Tchongo, ba shi kadai ya kitsa kai wannan farmaki ba, akwai wasu a gefe da suke taimaka masa.

Wannan ne karo na biyu a mako guda da aka yi yunkurin juyin mulki a kasashen yammaci da tsakiyar Afirka, inda a makon da ya gabata aka dakile irin hakan a kasar Saliyo. Tun daga 2020, an gudanar da juyin mulki sau 8 a yankin ciki har da jamhuriyar Nijar da Gabon a wannan shekara ta 2023.