An bude rumfunan zaben shugaban kasa a Chadi
May 6, 2024Mahamat Déby, ya hau kan mulkin kasar ta Chadi a 2021, bayan mutuwar mahaifinsa da ya mulki kasar tun daga 1990, zai fafata da tsohon Firaiministan kasar Success Masra, wanda ke kan gaba a adawa. Sauran 'yan takarar sun hada da tsohon Firaiministan kasar Albert Pahimi Padacke da wasu 'yan takarar guda bakwai.
Karin bayani: Fafutukar karshe ta yakin neman zabe a Chadi
An kashe babban 'dan adawar da ake hasashen cewa zai kasancewa shugaban kadangaren-bakin tulu Yaya Diallo, a birnin N'Djamena, a ranar 28 ga watan Fabrairu wato ranar da aka sanar da lokacin da za a gudanar da zaben shugaban kasar a hukumance.
Karin bayani: Chadi: An hana wasu 'yan adawa takarar shugaban kasa
Shugaba Mahamat ya tabbatarwa da al'ummar kasar cewa gwamnatin wucin-gadi zai yi domin dora kasar kan gwadaben dimukradiyya anan gaba, duk da cewa 'yan adawa sun yi watsi kalaman shugaban.