1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kokarin kawo karshen mulkin sojoji a Chadi

Dariustone Blaise
April 29, 2024

A Chadi 'yan takara goma ciki har da mace daya ke ci gaba da yakin neman zaben shugaban kasa da zai gudana ranar 6 ga watan Mayu.

https://p.dw.com/p/4fIWm
Hoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP

Sai dai wasu masu lura da al'amran siyasar Chadi suka ce 'yan takara ba su cika tabo ainihin matsalolin da ke ci wa al'umma tuwo a kwarya ba a lokacin da suke tallata manufofinsu na siyasa ba.

Fiye da makonni biyu 'yan takara suka shafe suna shiga sako da lungu na Chadi don neman hadin kan masu kada kuri'a a zaben shugaban kasa na 06 ga watan Mayun 2024. Sai dai muhimman batutuwa da suke ambatawa a gangamin yakin neman zabe da ma manufofinsu na na siyasa na da kusanci da juna. Shugaban gwamnatin mulkin soja da ya tsaya takara Janar Mahamat Idriss Deby Itno ga misali, ya yi nasarar kafa wata gamayya mai suna " Pour un Tchad Uni" da zummar mayar da hankali tare da yin kira ga hadin kai 'yan Chadi. Amina Priscille Longoh da ke zama jami'ar hulda da 'yan jarida na dan takara Deby Itno ta ce ya juma yana  nanatawa batun hadin kai a jawabansa.

Mahamat Idriss Déby Itno
Mahamat Idriss Déby ItnoHoto: Mikhail Metzel/dpa/AP/picture alliance

"Manufar da dan takararmu yake dauke da ita ba wai na mutum daya ne kawai ba, a'a, amma na babban kawancen hadin gwiwa mai suna "Pour un Tchad Uni" ne. Muna son hidimta wa al'umma don samun zaman lafiya da samar da kyakkyawan ci-gaba a kasarmu. Ga Mahamat Idriss Deby Itno , hadin kan al'ummar kasarmu na da mahimmanci kuma wajibi ne don tsaronmu da ke zama ginshiki na ci gabanmu."

Firayiministan Chadi kuma madugun adawa Sucés Masra , wanda ke samun goyon bayan kawancen "Justice et Egalité" ya yi imanin cewa ya zama dole a yi kwaskwarima ga tsarin shari'ar don sake samar da sabon tubalin gina kasar Chadi, kasar da ke fama da rashin adalci da rashin daidaito. 

"A cikin shekaru biyar masu zuwa, ya rage wa mutanen Chadi su yanke shawara idan suna son cewa adalci da daidaito da kuma mutunci ga kowane dan kasar Chadi sun zama wani tsari na bai daya. Ni dan takarane da ke neman magance zukatan da aka raunana, ni dan takara ne da ke neman hada kan 'yan Chadi a kan mahimman abubuwa: adalci da daidaito."

Wasu batutuwa da 'yan takara goma da ke zawarcin kujerar shugabancin Chadi ke tabowa a yakin neman zabensu, sun hada da ci gaba da hadin gwiwar kasa da kasa don kawo ci gaba, kuma tsohon firaministan kasar Pahimi Padacké Albert yana daga cikin wannan rukuni. A nasu bangaren, wasu 'yan takara biyu Lydie Beassemnda da Nasra Djimrangar suna da burin mayar da kasar Chadi a matsayin tarayya, lamarin da ya yi hannun riga da tsarin jamhuriya da ake dora kasar a kai tun bayan da ta samu 'yanci daga Turawan Faransa.

Amma dai masanin kimiyyar siyasa Evariste Ngalem Toldé ya ce idan aka duba yadda yakin neman zaben ke gudanawa, za a lura da cewa 'yan takara ba su yi magana a kan wasu muhimman batutuwa ba.

Tschad | Militärparade zum Unabhängigkeitstag | Mahamat Idriss Deby
Hoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP

"Ba a tabo ainihin matsalolin da kasar nan ke fama da su ba. Da farko idan aka yi magana a kan sojoji, babu wanda ya bayar da shawara sosai game da sake fasalin aikin soja. A fili yake cewa a yau sojoji ba sa a matsayi na tsaka-tsaki, kuma jami'an gwamnati kamar sojoji sun tsunduma dumu-dumu cikin harkokin siyasa. Kusan babu ma'aikata a dukan ofisoshi na gwamnati, lamarin da ke nunawa cewar komai ya tsaya cik. Sannan batun rarrabuwar kawuna tsakanin Kudu da Arewa ba dan takara da ya tabo."

A daidai lokacin da ya rage mako daya a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasar Chadi, yakin neman zaben ya zama tamkar wani dandali na yin musabaha tsakanin wasu ‘yan takara, lamarin da ya tilasta wa hukumar zabe (ANGE) kaddamar da kira na kauce wa tada zaune tsaye tare da bin ka'idojin zabe sau da kafa da kuma nuna kyakkyawan halaye a siyasance.