SiyasaGabas ta Tsakiya
Amurka za ta kara karfin soja a Gabas ta Tsakiya
August 3, 2024Talla
Ma'aikatar tsaro ta Pentagon, ta ce Amurkar za ta yi hakan ne domin hana rincabewar al'amura sakamakon barazanar da kasar Iran da masu alaka da ita ke yi na yiwuwar kai hare-hare.
Tun bayan kazamin harin ranar bakwai ga watan Oktoba da kungiyar Hamas ta kaddamar a kan Isra'ila da ya yi sanadin yakin da ake ciki a Gaza ne dai Sakataren Tsaron Amurkar Loyd Austin ya jadda shirin Amurka na kare mutane da muradunta a yankin.
Rikici dai na kara kazanta a yankin Gabas ta Tsakiya, bayan kisan jagoran kungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Iran da ma wani babban kwamandan Hezbollah a Beirut babban birnin kasar Labanan.